Mika hannun zumunci da kasar Koriya Ta Kudu ta yi a gasar Olympic, ya haifar da wani cigaba a diflomasiyyance a yau dinnan Asabar, ta yadda har sai da aka gayyaci Shugaban Koriya Ta Kudun Moon Jae-in ya gana da Shugaban Koriya ta Arewa a Pyongyang.
Kim Yo Jong, ‘yar’uwar Shugaban Koriya Ta Arewa, ita ce ta mika ma Shugaba Moon wata wasika mai bayyana dalla-dallar niyyar Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ta inganta dangantakar Koriyawan, a yayin liyafar cin abinci na tawagar gasar Olympics na kasar Koriya Ta Arewa a ginin Fadar Shugaban kasar Koriya Ta Kudu. A cewar kakakin Fadar Shugaban Koriya Ta Kudu Kim Eui-Kyeom, da baka ‘yar uwar Kim din ta isar da sakon gayyatar Shugaba Moon Jae-in, ya gana da Shugaban Koriya Ta Arewa a Pyongyang a duk lokacin da zai iya zuwa.
A cewar Kim, “Shugaba Moon ya bayyana aniyarsa ta ganin wannan ganawar ta yiwu, ta wajen samar da yanayin yin haka nan ba da dadewa ba.”
Wannan gayyatar ta bude kofar ganawa a karon farko cikin shekaru 10 tsakanin Shugabannin Koriya Ta Arewa da Koriya Ta Kudu.