Shugaban Kenya Ya Bayyana Bakin Cikinsa a Kan Kashe Babban Jami'in Hukumar Zabe

Shugaban Uhuru Kenyata na Kenya

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya yayi amfani da kafofin sada zumunta na yanar gizo inda ya bayyana "bakin cikinsa" kan kashe wani babban jami'in hukumar zabe, gabannin zaben kasar da za'a yi makon gobe.

Shugaba Uhuru yayi amfani da dandalin Facebook da Twitter yayi kira a tabbatar da cewa binciken kisan da aka yiwa Christopher Msando, "ya ci gaba cikin tsanaki" ba tareda wani cikas, ba a dai dai lokacinda wasu mutane masu yawa suka yi maci zuwa ofishin hukumar zaben dake tsakiyar birnin Nairobi, suna neman ganin an yi adalci.

Msando, wanda kafin mutuwarsa, shine jagoran bangaren na'urarorin komputa a hukumar zaben kasar.Yayi kokari ya tabbatarwa 'yan kasar cewa ba za'a yi aringizo ko katsalandan da sakamakon zaben ba.

Ranar Litinin ne aka ga gawarsa, bayan da ya bace tun ranar Jumma'a. Kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar ya fada, sai da aka gallazawa Msando ukuba kamin a kashe shi.