Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh yace ba zai sauka daga karagar mulki ba muddar tsohon abokin hamayyarshi, wani babban janar da ya balle ya shiga jam’iyar adawa da kuma hamshakin mai kudin nan shugaban kabilu da iyalinshi suna ci gaba da tasiri da ikon fada a ji a kasar.
A cikin hira ta musamman da jaridar Washington Post da kuma mujallar Time suka yi da shi, Mr. Saleh yace tsarin mika mulkin da kasashen yankin Gulf dake makwabtaka da Yemen suka shata yace a kawar da duk wadanda suke ruruta wutar rikici a kasar.
Bisa ga cewarshi, wannan yana nufin ba zai mika mulki ba muddar janar ali Mohsen al-Ahmar da kuma Hamid al-Ahmar, wani hamshakin dan kasuwa a harkar sadarwa, wanda dan’uwanshi ke shugabancin tarayyar kabilu mafi karfi a kasar Yemen, suna da ‘yancin tsayawa takara.
Mr. Saleh ya yi gargadi da cewa, kyale mutanen biyu su ci gaba da rike mukamansu bayan ya yi murabus yana da hadarin gaske, bisa ga cewarshi, sakamakon zai iya tsunduma kasar cikin yakin basasa. Ya zargi abokan hamayyarshi na siyasa da fakewa da tarzomar da ake yi a kasar Yemen wajen tilasa mashi barin shugabanci.
Mr. Saleh ya kuma bayyana cewa, yana yiwuwa kabilar janar da kuma Ahmar sun taka rawa a harin da aka kaiwa fadarshi cikin watan Yuni inda aka ji mashi mummunan rauni.