Hukumar zaben Venezuela ta ba da sanarwa cewar shugaban kasar da ke kan mulki Nicolas Maduro ya sake lashe zaben da aka kamala, abinda zai bashi damar ci gaba da zama akan karagar mulkin har na tsawon karin wasu shekaru 6 a karo na biyu.
‘Yan adwa sun kauracewa zaben wanda aka gudanar a ranar Lahadi wanda suka kira rantsar da mugun shugaba wanda kuma kasashen duniya sukayi Allah wadai dashi.
An saka ran cewa Maduro, dan shekaru 55 wanda kuma tsohon direban hayis ne zai lashe zaben, duk da cewa akwai rikici da yake ta zurfafa har ya sanya kayan abinci sukai karanci a yayin da samar da man fetur yayi kasa a kasar wacce take daya daga cikin manyan kasashe masu fitar da mai ta duniya.
Wani tsohon gwamna a kasar, Henri Falcon shine yayi takara da Maduro amman fitowar wani Fadan coci Javier (Haviya) Bertuce ya taimaka wajen hana shi samun nasara.