Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, zai isa kasar Qatar, a wata ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun bayan gagarumar zanga zangar nuna wa gwamnatinsa adawa da aka yi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Qatar(QNA) ya bada rihoto cewa a gobe Laraba ne shugaba Bashir zai gana da sarkin Qatar Sheik Tamim bin Hamad Al Thani domin tattaunawa akan yadda za su bunkasa dangantaka tsakaninsu.
Shugaba Bashir ya ki ya dau zanga zanagar da muhimmanci, ya dage cewa wasu ‘yan tsirarun mutanen kasashen waje da magoya bayansu ne suke ingiza wutar rikicin.
Tun daga ran 19 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ne Kasar Sudan ta soma fuskantar zanga zangar jama’a, bayan da gwamnati ta kara farashin brodi.
Adawar da ake nuna wa gwamnatin ta na dada karuwa, har mutane da yawa ta neman sai a kawo karshen gwamnatin Shugaba Bashir da ta kwashe shekaru talatin kan karagar mulki.