Shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou ya kaddamar da katafariyar kasuwar zamani a garin Damagaran mai suna Dole.
Ministan cikin gidan kasar Bazoum Muhammad ya yi bayani bayan an bude kasuwar. Ya ce shekara daya da ta wuce lokacin da aka fara gina kasuwar an samu cecekuce. Wasu mutane sun nuna shakkun gina irin wannan kasuwa da irin alherin da za ta yi. Ya ci gaba da cewa babbar kasuwa ce kuma za ta dauki duk mutanen dake son bude shaguna. Baicin haka an yi mata ginin zamani tare da sa kaya na zamani.
Inji ministan kasuwar nada tsaro. Ya ce babbar kyauta ce da shugaban kasa ya yiwa Zinder saboda kasuwar dake wurin da can da zara an yi ruwa ba'a iya shigarta amma sai gata yau ta zama ta zamani. Kasuwar za ta kawowa tattalin arzikin jihar bunkasa.
Kasuwar tana dauke da shaguna 2152 da duk abubuwan more rayuwa da ake bukata a kasuwa.
Alhaji Babakir Muhammad shugaban 'yan kasuwan ya ce yana kunshe da farin ciki da Allah ya sa aka gina kasuwar aka kuma kaddamar da ita. Haka ma al'ummar gari suka bayyana farin cikinsu da samun kasuwar.
Ga rahoton Tamar Abari
Your browser doesn’t support HTML5