Shugaban kasar Liberiya George Weah, yayi shiri domin karrama tsohon kocinsa, Arsène Wenger, da lambar yabo mai daraja a kasar.
Wenger ne ya sayi Shugaba George Weah, a lokacin da yake taka leda wanda ya kasance shi ne kadai dan wasan kwallon kafa daga Afirka da ya lashe kyautar dan kwallon duniya, a shekarar 1988, lokacin Wenger yana kocin kungiyar Monac,o dake kasar Faransa.
Koc Wenger, wanda a kwananne ya ajiye aikinsa a kungiyar Arsenal, bayan ya shafe shekaru 22 a matsayin koci, a yayin da yake Kocin ya sayi 'yan wasan Afirka da dama da suka buga wasa a karkashin sa.
Shi kuwa George Weah, ya yi ritaya daga buga wasan kwallon kafa a shekara ta 2003 inda ya fada cikin harkokin siyasa. Ya samu nasarar lashe zaben da a ka yi a Liberiya, a shekarar da ta gabata da gagarumin rinjaye.
A yayin hirarsa da manema labarai, ministan watsa labarai na kasar Liberiya, Eugene Nagbe, ya shaida wa manema labarai cewa ana sa ran Wenger, zai isa Monrovia, babban birnin kasar a ranar Asabar domin karbar lambar yabo daga shugaban kasar Laberiyan George Weah.
Your browser doesn’t support HTML5