Sabon Firayim Ministan Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya ce tsaron lafiyar 'yan kasar na daga cikin manyan abubuwan da zai sa a gaba.
WASHINGTON DC —
Bayan nadin Sama Lukonde Kyenge da Shugaba Felix Tshisekedi ya yi a ranar Litinin, ya ce tsaro zai kasance daya daga cikin bangarorin da za a bai wa mahimmanci, musamman a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma lardin Katanga.
Ya kuma kara da cewa za ta hada da karin matasa da mata cikin gwamnatinta.
Sama Lukonde ya fara sabon aikin nasa ne bayan ya shugabanci kamfanin hakar ma'adanai kuma a baya ya shugabanci ma'aikatar Matasa da Wasanni.
Ya maye gurbin Sylvestre Ilunga Ilunkamba, wani dan hannun damar tsohon shugaban kasar Joseph Kabila, wanda ya sauka daga mukaminsa a watan da ya gabata bayan kada kuri’ar rashin amincewa da majalisar.