Da yake bayani wa manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugaban kasar Niger shugaban kamfanin ORANO, tsohuwar AREVA PHILIPE KNOCHE ya bayyana cewa sun tanttauna akan batutuwan da suka shafi huldar bangarorin biyu wace ta ta’allaka akan aiyukan hakar ma’adinin uranium kuma kamfanin ya samu lambar yabo akan maganar kare mahalli a yankin AGADES abinda shugabar kungiyar GREN HAJIYA RAMATOU SOLI ke kallonsa tamkar almara.
Ta ce duk wanda aka fada masa cewa an ba kamfanin Orano lambar yabo akan muhalli dariya za’a yi masa. Kura da dattin da aka tara shekara da shekaru suna nan jibge. Rashin dasa itatuwa da rashin ruwan sha har yanzu suna damun mutanen yankin.
Bayan birnin Yamai shugaban kamfanin ORANO ya ziyarci wuraren da kasar FARANSA ke hakar uranium a karkarar ARLIT saboda haka masu kare hakkin jama’a ke cewa shugaban ya kamata ya samu damar gani da idanunsa halin kuncin da kamfaninsa ya jefa jama’a ciki sabanin abinda yarjejeniyar 2014 ta tsayar.
Mai fafutikar jama’ar yankin Alit, musamman mata suna shan wuya da batun ruwa. Cikin tsakar dare suke layi bakin famfuna su samu ruwan da bashi ma da tsaftar sha. Koda shugaban kamfanin bai sha ba ya kai a gwada domin ya tabbatar cewa ba kage ake yi ba.
Faduwar darajar karfen uranium a kasuwannnin duniya ta haddasa korar ma’aikata da dama daga aiki a rassan ORANO dake Niger wato SOMAIR da COMINAK sai dai a ra’ayin shugaban kungiyar AEC, MOUSSA TCHANGARI girman matsalar bai kai mizanin da za a dauki irin wannan mataki ba.
Moussa Tchangari ya ce an ba kamfanin Orano komi amma sai ya kori ma’aikata. Ya bata hanyoyi da muhalli amma bai hana kamfanin zuwa ya yi karya ba. Bugu da kari an dauka kamfanin yana taimako ne har ana cewa ya na jin tausayin kasar ne da yake sayen karfen uranium.
Shugaban kamfanin ORANO wato tsohuwar AREVA PHILIPE KNOCHE ya ce an dan fara samun tashin farashin uranium a kasuwannin duniya yayinda batun nuclear ke ci gaba da haddasa mahawara saboda dalilai masu nasaba da dumamar yanayi. Ya bayyana aniyarsa ta karfafa tallafi domin bunkasa aiyukan noman rani dai dai da alkawalin da suka yi wa jama’ar yankin AGADES musamman a fadamar IRAZHER .
A saurari rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5