Shugaban hukumar lamuni ta duniya Christine Lagard ke Magana bayan ta gana da shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar wuni 4 da ta kawo Najeriya.
Lagard taci gaba da cewa mun tattauna batun raguwar farashin mai da shugaba Buhari da hanyoyin natsuwa wajen tafiyar da lamurran kudi don biyan bukatun karuwar yawan mutane ta hanyar matakai na dogo da gajeren zango .
Tace hakan kuma zaiyi nasara ne ta hanyar gano hanyoyin kudin shiga na cikin gida
.Shugaban tace bata zo Najeriya don bada lamuni ba amma tana goyon bayan hanyoyin tattalin arziki da zasu samar da kudi domin gudanar dakasafin kudi.
Sai dai da ‘yan jarida suka tambaye ta kome yasa kasashe masu tasowa ke kara talaucewa akan ka’idojin hukumar bada lamunin?
Ga Madina Dauda da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5