Injiniya Ahmed Yusuf yace a ka'idar shari'a abun da ya fi kyau shi ne a ba mutum hakinsa ba tare da yin wata wata ba.
Yace ciyar da al'umma yana da kyau amma basu hakinsu shi ne ya fi alheri maimakon a basu wani abu kamar kyauta. Kullum kamata yayi mutum ya sauke nauyin dake kansa ba yin kyauta ba.
Yace saboda haka yana ba gwamnatin Bauchi shawara cewa don Allah ta duba nauyin dake kanta, a ragewa ma'aikata nauyin albashinsu da masu fansho da makamantansu koda ma ba za'a iya biyansu duk abun da suke bin gwamnati ba.
Yin hakan shi ne ya fi karbuwa ga Allah maimakon a dauki kudin da aka kwato daga wadanda suka wawuresu a bi wata hanya dasu.
Amma ta bakin kwamishanan addinai da zamantakewa na jihar Bauchin Alhaji Abdullahi Muhammad Idris, yace gwamnati bata dauki kudin ma'aikata ba domin ciyar da mutane abincin bude baki. Haki ne akan gwamnati ta ciyar da irin wadannan rukunan jama'a da basu da karfin ciyar da kansu lokacin azumi. Yace gwamnati ta fara biyan albashi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5