Cecekucen da ya mamaye kafofin labaran kasar Ghana akan wata yarjejeniyar soji da aka ce Ghana ta kulla da Amurka, ya sa shugaban kasar ya fito ya yiwa jama'a jawabi.
Shugaba Akufo Addo ya nuna cewa kokarin gwamnatinsa na barin al'ummar kasar ta san abun da gwamnati ke yi ya jawo cecekucen saboda gwamnatocin baya sun kulla irin yarjejeniyar, amma a wancan lokacin ba'a bari jama'ar kasar sun sani ba.
A 1998 da shekara ta 2000 da 2015 an kulla irin yarjejeniyar amma saboda munafunci wadanda suka yi hakan can baya yanzu su ne suke fadan za'a sayar da 'yancin Ghana wa Amurka. A cewarsa hakan ba zai taba aukuwa a karkashin mulkinsa ba.
Can baya an kula yarjejeniya da Amurka domin zaman lafiya balantana yanzu da rigingimu da fitintinu suka fi yawa musamman ta'addanci a kasashen dake makwaftaka da Ghana. Shugaba Akufo yace domin tabbatar da tsaron kasa da samun zaman lafiya ya ga mahimmancin kulla yarjejeniyar da Amurka da zummar taimakawa sojojin kasar.
Mr. Nana Akufi ya ci gaba da cewa,kasarsa bata kulla yarjejeniyar kafa sansanin soja da Amurka ba cikin kasar. Ita ma kasar Amurka bata gabatar da bukatar yin hakan ba.
Sai dai wani dan majalisa daga jam'iyyar adawa MBC bai yadda da bayanan shugaban ba saboda wai ko yarjejeniyar da suka gabatar wa majalisa babu hannun shugaban ciki ko na wani ministan kasar. Ya ce abun da ya dame su shi ne sojan Amurka na iya shiga Ghana amma dokar kasarsu ba zata yi aiki a kansa ba kowane irin laifi ya aikata. Idan sun kafa sansani babu abun da Ghana zata yi domin bata da ikon shiga ciki.
Ga rahoton Ridwan Abbas da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5