Sakamakon binciken da kwamitin da babar akaliyar kasar Justice Sophia Akuffo ta kafa wanda ya binciki muna munan da aka zargi hukumar zaben kasar da yi, ya sa shugaban Ghana ya sallami shugabar hukumar da wasu na hannun damanta biyu.
Al’ummar kasar suka koka da shugabar hukumar zaben da mataimakan ta biyu. Kwamitin binciken ya bada shawarar a sauke su daga mukaman su saboda halayar da suka nuna da kuma rashin iya aiki.
Cikin karar da aka yi akan su akwai yin amfani da kudin kasar miliyan uku da digo tara ba akan ka’ida ba. Sun kuma yi amfani da dalar Amurka miliyan 14 alhali kuwa an basu izinin yin amfani da miliyan bakwai da rabi ne kawai.
Ministan labaran kasar Mustapha Abdulhamid ya fada cewa shugaban kasa ya umurci mutanen uku su mika duk abun dake hannunsu mallakar gwamnati ga dakaktan hulda da mutane na hukumar.
To saidai babbar jam’iyyar adawar kasar, NBC ta kalli abun ta wata fuska dabam. Ba tare da bata lokaci ba ta kira wani taron manema labarai domin bayyana rashin amincewa da matakin da gwamnati ta dauka. Tace salamar jami’an, wani shiri ne na neman yin magudi a zabe mai zuwa. Suna cewa idan basu da shirin satar zabe ba zasu kori mutanen ba. Jam’iyar yau Juma’a jama’a zasu fito su nuna fushinsu da matakin da gwamnati ta dauka.
Mai magana da yawun jam’iyar NBC, yace duk jam’iyyun adawa zasu yi taro domin tsayar da shawara akan matakin da zasu dauka. Suna son a bayyana masu dalilin da ya sa aka sallami shugabar hukumar zabe da mataimakan ta biyu.
A saurari rahoton Ridwan Abbas domin jin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5