Shugaban kasar Ghana ya sallami ministan makamashin kasar, Boakye Agyarko daga mukaminsa.
Duk da cewa bai bayyana dalilin ko dalilan da suka sa ya sallameshi daga aiki ba masu kula da harkokin kasar, suna zargin cewa ministan na da hannu dumu-dumu cikin wata muna-munar da aka yi a harkar man fetur din kasar.
Sakataren ma'aikatan man fetur na kasar ya yabawa shugaban kasar inda ya ce hakika shugaba Akufo Addo ya yi adalci da korar ministan. Ya ce tun daga watan Fabrairu suke kira a tsige ministan saboda yin rufa-rufa da sanya hannu a wata yarjejeniyar hakan man fetur da ya cutar da kasar.
A cewar masu ruwa da tsaki a harkar kasar yanzu kam sun tashi ba za su bari a yi masu dodorido ba musamman a harkar man fetur a kasar.
A saurari rahoton Ridwan Abbas da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5