WASHINGTON D.C. —
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta wayar tarho, inda ya bayar da hakuri kan rushe ginin ofishin jakadancin Najeriya da aka yi a Ghana.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar gwamnatin Najeriya mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnatin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.
A yayin wayar tasu, shugaban na Ghana ya fadawa Buhari cewa ya sa a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cewar sanarwar, da safiyar yau Talata ma, an kama wasu wadanda ake zargi da hannu a lamarin kuma za a gurfanar da su a gabatan kotu.