Kasar Faransa na gudanar da biki yau Laraba domin girmama wani jami’in dan sanda da aka kashe a satin da ya gabata bayan ya mika kansa garkuwa ga wani dan bindiga a maimakon wasu da aka yi garkuwa da su a yayin wani hari da aka kai a wani babban kanti.
Shugaba Emmanuel Macron zai yi jawabi a bikin da ake a birnin Paris don karrama Lt. Col. Arnaud Beltrame wanda ya ba da kansa garkuwa.
Shugaban ya ce, Beltrame ya mutu jarumi.
A safiyar yau Laraba ne, ma’aikatun ‘yan sanda a fadin kasar, suka dakata suka yi shuru na minti daya ba magana biyo bayan yin shuru da ‘yan majalisar dokokin kasar suka yi jiya Talata.
Dan bindigan da ya kai hari ranar juma’a ya kashe wasu mutane uku.
Hukumomi sun gano cewa wani dan shekara 25 ne dan asalin Faransa da Morocco mai suna Radouane Lakdim, kuma tuni kungiyar ‘yan ta’addar ISIS ta dauki alhakin kai harin.