Shugaban Majalissar Sojojin da ke mulki a Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya gana da shugabanin kungiyoyin fararen hula magoya bayan CNSP a karshen mako domin tantauna halin da kasar ke ciki watanni kusan 10 bayan juyin mulkin da ya jagoranta.
Kungiyoyin da suka hada da Front Patriotique da M62 da sauran kawayensu masu goyon bayan manufofin CNSP a wannan ganawa sun soma ne da jin ta bakin shugaban majalissar CNSP Janar Tiani a game da yadda sha’anin mulki ke gudana a kasar.
Tsadar rayuwa da matsalolin tsaro na daga cikin batutuwan da aka tattauna akansu a wannan zama wanda a yayinsa aka kwatanta cewa lokacin bullo da ajandar tafiyar da al’amuran mulkin rikon kwarya bai yi ba.
A na su gefe kungiyoyin sun gabatar da koken al’umma donganin hukumomi sun dauki mataki a kai.
Kan maganar tafiyar da lamuran gwamnatin rikon kwarya da shirin bullo da ajandar zabe shugaban majalissar CNSP ya gaya wa ‘yan farar hula cewa a jira lokaci inji Bana Ibrahim na FP.
Wasu ‘yan fafutika da ake yi wa kallon masu farfagandar yada manufofin Rasha wadanda suka hada da Kemi Seba dan asalin jamhuriyar Benin da Nathalie Yamb ‘yar asalin kasar Cameroun da suka zo takanas daga Turay sun kudiri aniyar gudanar da gangami a biranen Agadez da Zinder a ranekun asabar da yau litinin da nufin zaburar da ‘yan Nijer akan maganar kin jinin manufofin kasashen yammacin duniya.
Sai dai daga bisani an bada sanarwar soke taron ba tare da bayyana wani dalili ba koda yake ana ganin korafe korafen da ‘yan fafutikar cikin gida suka yi kan zuwan wadanan mutane ya sa wadanda suka gayyato suka canza ra’ayi.
A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5