Yayinda yake jawabi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya shugaban China Xi Jinping ya sha alwashin goyon bayan shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya
WASHINGTON DC —
Shugaban kasar China Xi Jinping ya sha alwashin marawa zaman lafiya baya, tare da rungumar ci gabanduniya da kuma yunkurin rage dumamar yanayi.
Ya fadi haka ne lokacin da yake bayani ga shugabanin kasashen duniya a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a New York ta nan Amurka.
Ya yi alkawarin bada gudunmawar dalar Amurka Biliyan 1 ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na zaman lafiya da ci gaba. Ya kuma yi alkawarin kirkiro sojoji da zasu maye gurbin kimanin 8000 na rundunar wanzan da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.