Shugaban China Ya Isa Afirka Don Fadada Harkokin Cinakayya

  • Ibrahim Garba

Shugaba Xi (Shi) Jingping

A ciagaba da kokarin yin kane-kane a Afrika ta fuskoki dabandaban, Shugaban China Mr. Shi (Xi) Jingping ya isa nahiyar inda zai fadada harkokin kasuwanci da diflomasiyya da wasu kasashen na Afrika.

Shugaban China Xi (Shi) Jinping ya fara ziyarar aiki a kasashen Afirka hudu daga jiya Asabar, inda ya isa kasar Senegal.

Ana kyautata zaton Mista Shi zai rattaba hannu kan yarjajjeniyar cinakayya ta bai daya da Senegal, wadda ke da tattalin arziki mai saurin habbaka.

Tuni kasar ta China ta shiga saka jari da bayar da basussuka da kuma shiga yarjajjeniyoyi da kasashen Afirka don ta baza madahunta, ta kuma samu kaiwa ga albarkatun karkashin kasa na Afrika da kuma kasuwannin Afirka masu muhimmanci ga tattalin arzikinta.

Mr. Shi zai kuma ziyarci kasashen Rwanda da Mauritius da kuma Afirka Ta Kudu.