Ma’iakatar yada labaran gwamnatin China ta ce, Xi zai ziyarci ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya tare da binciken kokarin da ake yi na dakile barkewar cutar.
Ziyarar na zuwa ne a lokacin da jami’an lafiya suka ce an samu sababbin wadanda suka kamu 19 a yau Talata, lamarin dake nuna ana ci gaba da samun raguwar yaduwar cutar a China, yayin da cutar ke kara yaduwa cikin gaggawa a wasu kasashe. An riga an shawo kan kimanin kashi 70 cikin dari na cutar a China.
A cikin matakan da ta dauka, China ta rufe manyan wurare domin dakile yaduwar cutar a manyan tarukan jama’a ko kuma tsakanin matafiya da zasu tafi wasu wurare a cikin kasar.
Kasar Italiya ita ma tana daukar irin wannan mataki bayan da ta zama daya daga ciki kasashen da cutar tayi tsananin bazuwa bayan kasar China, inda mutane sama da dubu tara suka kamu kana wasu dari hudu da sittin suka mutu.