Xi Jinping ya kasance shugaban China na farko da ya ziyarci kasar Nepal sama da shekaru 20 da suka wuce, ana sa ran shugaban zai sanya hannu a wasu yarjejeniyoyi akan manyan ayyukan gina kasa da yawa a ziyarar ta sa.
A jiya Asabar Xi ya isa kasar daga India, inda ya gana da Firayin Minista Nerandra Modi. Ana kuma sa ran Nepal zata yi taka-tsan-tsan a yayin da ta ke kulla dangantaka da manyan kasashe makwabtanta wato India da China.
India na taka rawa a wurare daban dabam a harkokin tattalin arzikin Nepal da siyasar kasar, yayinda China da Nepal suka hada iyakar dake kewaye da manyan tsaunuka.
Jiang Zemin shi ne shugaban China na karshe da ya je Nepal kafin Xi, a shekarar aluf dari tara da cisi’in da shida.
Shugabar Nepal Bidhya Devi Bhandari da Firayin ministan kasar K.P Sharma Oli ne suka je tarbar Xi a tashar jiragen saman Kathmandu.