Shugaban mulkin sojan kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby yace zai mutunta duk sakamakon daya bayyana a karshe, wanda ake ganin ba zai bambanta da kwarya-kwaryan sakamakon da aka wallafa a Lahadin data gabata wanda ke nuna cewar masu kada kuri’ar sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar dake tsakiyar nahiyar Afrika da kaso 86 cikin 100.
Deby ya bayyana haka ne a tashar talabijin din kasar a makon da muke ciki bayan da ayyana kwarkwaryan sakamakon kuri’ar raba gardamar.
A ranar Alhamis din nan kotun kolin kasar Chadi zata ayyana sakamakon karshe akan kuri’ar raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar da zai share hanyar komawa ga mulkin farar hula.
Kwarya-kwaryan sakamakon ya bayyana cewar, al’ummar da suka kada kuri’ar sun amince da sabon kundin tsarin da kaso 86 cikin 100.
Rahoton hukumar CONOREC ya bayyana cewar fiye da kaso 63 cikin 100 na sama da masu kada kuri’a milyan 8.3 a kuri’ar raba gardamar data gudana a ranar 17 ga watan Disamba.
Sai dai jagororin ‘yan adawa da kungiyoyin fafutukar farar hular kasar Chadi na cewa galibin masu kada kuri’ar basu fito ba.
Jam’iyyun adawa, da suka hada da UDDP, sun bada rahoton cewar miliyoyin masu kada kuri’a basu ma karbi katunan zabensu ba.
Gabanin kada kuri’ar, hukumar zabe ta CONOREC ta bada rahoton cewar ta kaddamar da gangamin wayar da kan masu kada kuri’ar da suka cancanci yin zabe akan su karbi katunan zaben nasu.