Shugaban Amurka Barack Obama zai karbi bakuncin shugabannin Afirka a wani taro na kokarin inganta huldar cinakayya da saka jari da nahiyar.
WASHINGTON, DC —
Baya ga batun cinakayya, a cewar Fadar ta White House, Mr. Obama zai yi amfani da damar wajen jaddada alwashin da Amurka ta sha na tabbatar da tsaro da inganta demokaradiyya a Afirka.
Nan take dai ba a bayyana shugabannin Afirkan da za a gayyata taron ba.
Fadar White House ta bayar da sanarwar shirin taron a jiya Talata, da cewa za a yi ne a ranakun 5 da 6 ga watan Augusta a nan birnin Washington.