Shugaban Amurka Zai Kai Ziyara Orlando Inda Omar Mateen Ya Kashe Mutane 49

Jiya Litini Shugaban Amurka Barack Obama, ya ce babu wata shaidar cewa maharin nan da ya aikata kashe-kashen tarin jama'a mafi muni a tarihin Amurka, a wata mashakatar-dare ta 'yan luwadi da ke Orlando, jihar Florida, ya samu umurni daga wata kungiyar ta'addanci ta kasar waje.

"Da alamar tsauraran ra'ayoyin da ake yadawa ta kafar internet, su ne su ka ingiza maharin," a cewar Obama ga manema labarai a Fadar White House.

Ya ce maharin, mai suna Omar Saddiqui Mateen, dan shekaru 29 da haihuwa, wanda Ba'amarike ne Musulmi, wanda iyayensa su ka fito daga Afghanistan, wani nau'i ne na tsattsauran ra'ayin cikin gida da mu ka dade mu na fama da shi." a cewar Obama, wanda ya kara da cewa, "da alamar a karshe ne ya bayyana mubaya'arsa" ga kungiyar ISIS lokacin da ya buga wayar gaggawa ta 911 a Orlando.

Obama ya ce har yanzu jami'an tsaro na mataki na farko na bincike kuma, kamar yadda ya ce, "har yanzu akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu tabbatar."

Fadar ta White House ta ce Shugaba Obama zai je Orlando ranar Alhamis don ya "mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma nuna ya na tare da wannan al'ummar a daidai lokacin da su ke kokarin murmurewa."

Shugaban hukumar bincike ta FBI James Comey, ya ce, "Mu na nazarin raruwar makashin," ciki har da amfani da yanar internet da ya yi.

Da ya ke jawabi kwana guda bayan kisan na mutane 49 da bindiga a mashakatar dare mai suna Pulse inda wasu mutanen 53 su ka jikkata, Obama ya ce maharin ya sayi makaman ne kan ka'ida. Ya ce daya daga cikin makaman da ya yi amfani da su wata bindigar hannu ce mai kunamu da yawa." Hukumomi sun ce Mateen, wanda 'yan sanda su ka kashe shi daga baya, ya yi ta luguden wuta da wata bindiga mai sarrafa kanta.

"Bai fuskanci wata matsala wajen sayen wadannan irin makaman ba," a cewar Obama, wanda ya sha kokarin ganin an kafa dokoki mafiya tsauri kan mallakar bindiga a Amurka amma bai yi nasara ba.

Omar Mateen wanda ya yi kisan gilla a Orlando