Shugaban Amurka ya yi nazari akan wa'adin mulkinsa

Shugaban Amurka Barack Obama

Yayinda yake duba baya a wa'adin mulkinsa shugaban Amurka Barack Obama ya ambato kasar Libya a matsayin wata kasa inda ya yi kuskure saboda rashin tanadin wani shiri da zai maye gurbin gwamnatin Moamar Gaddafi

Shugaban Amurka Barack Obama yace gaza shirya wani kwakwaran matakin da za'a dauka bayan an hambarar da shugaban Libya Moammar Gaddafi shi ya zama babban kuskure da ya yi a shugabancinsa..

Shugaban ya yi wannan furucin ne yayainda yake duba baya akan nasarori da ya samu a shugabancinsa da kuma wuraren da ya gaza a gwamnatinsa.

Shugaba Obama ya fadawa Chris Wallace wanda ya yi fira dashi ta kafar talibijan yace shiga kasar Libya domin kare fararan hula yana kan ka'ida. Barin kasar cikin rudani bayan kasarsa da kawancen NATO sun kashe shugaban Libya Moammar Gaddafi babban kuskure ne lamarin da ya bar kasar cikin mugun rudani da har yanzu take fama dashi.

Shugaban ya ambato ranar da majalisar dokokin ta amince da shirin nan nasa na kiwon lafiya da aka lakawa suna Obamacare tamkar ranar da ta fi bashi farin ciki saboda kowane ba'amarike zai iya samun insurar kiwon lafiya a saukake.

Haka kuma shugaban ba zai taba mantawa da ranar da ya kai ziyara garin Newton ba , wani karamin gari a jihar Connecticut kwanaki biyu bayan wani dan bindiga ya kashe yara kanana ishirin da malamai shida. Ranar ta zama masa ranar mugun bakin cikin da har abada ba zai manta da ita ba.