Shugaban Amurka ya yada zango a Landan kasar Birtaniya

Shugaban Amurka Obama da Sarauniyar Ingila da matar shugaban

A kan hanyarsa ta dawowa gida daga ziyarar da ya kai kasar Saudiya shugaban Amurka da matarsa sun yada zango a Landan domin su taya Sarauniya Ingila murnar cika shekaru casa'in da haihuwa a duniya

Bayan taya Sarauniyar Ingila murnar cika shekaru casa'in da hahuwa shugaba Obama zai yi shawarwari da David Cameron Firayim Ministan Ingila.

Shawarwarin zasu kasance ne akan yunkurin dakile ta'adanci da rikicin 'yan gudun hijira da kasashen turai ke fama dashi. Akwai kuma batun matsalar tattalin arzikin duniya da yanzu yake tanga tanga.

Shugaban Amurkan ya isa Ladan ne bayan da ya halarci taron koli na kungiyar kasashen yankin Gulf da ake kira GCC a takaice. An yi taron ne a kasar Saudiya inda shugaban yace Amurka da shugabannin yankin bakinsu ya zo daya akan yaki da kungiyar ISIS da kuma daidaita alamura a yankin gabas ta tsakiya wadda take fama da rikici..

A taron, kasashen yankin Gulf din da Amurka sun amince da bukatar magance rikicin Syria a siyasance.