Mr. Obama yace za'a iya auna irin ci gaban da aka samu a taron kolin ta wajen auna yadda matakai da suka dauka ya kawar da damuwa da za'a shiga, da kuma kare duniyar baki dayanta.
Mr. Obama yace shugabannin kasashen da suka hallara a taron kolin duk sun fahimci bukatar a dauki matakan gaggawa na rage hayaki daga na'urori masu amfani da man fetur da danginsu. Ya bada misali da irin ci gaban da aka samu a Amurka da ma wasu kasashe.
A nasa jawabin, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, yace tilas ne "taron kolin ya yanke shawara mai ma'ana, kuma shugabannin suna da ikon daukan matakai da zasu kare wannan zamani dama mai zuwa.
Ahalinda ake ciki kuma,Amurka da China kasashe biyu da suke da masana'antu da suka fi gurbata yanayi sun sake nanata kudurinsu na daukan matakai d a zasu rage hayaki mai gurbata muhalli. Sun nanata hakan ne a taron koli da ake yi kan sauyin yanayi.