Shugaba Donald Trump ya jingine barazanar da ya saba yi wa Korea ta Arewa, inda a jiya Talata ya gabatar da wani jawabin kara kwarin gwiwa ga Korea ta Kudu, yana mai cewa, “za a samu mafita” dangane da barazanar da hukumomin Pyongyang ke yi na makamin nukiliya.
Bayan kwashe yinin da ya yi yana wasu tararruka da bayyana a baina jama’a tare da shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in a Birnin Seoul, shugaba Trump, ya ce an dauki matakan diplomasiyya wajen yayyafa ruwan sanyi kan takaddamar da ta dabaibaye yankin na Korea.
Wadannan kalamai na Trump sun sha banban matuka da sakonnin Twitter da ya rika wallafawa a ‘yan makwannin bayan nan, inda ya rika nanata cewa hawa teburin tattaunawa da hukumomin Pyongyan domin nemo bakin zaren takaddamar mallakar makamin nukiliyan, duk bata lokaci ne.