Firaim ministan kasar Japan Shinzo Abe yace shugaba Trump ya fahimci irin lamarin nan dake sosawa al’ummar kasarsa rai, da ya shafi yadda jami’an Koriya ta arewa suka shafe shekaru suna sace al’ummar kasar.
Yace shugaba Trump ya bayyana cewa za a yi iyaka iyawa a warware matsalar.
A nashi bangaren kuma shugaba Donald Trump yace, “muna tattaunawa yanzu haka” domin ceto Amurkawa uku da Koriya ta Arewa take tsare da su, sai dai bai bayyana ko ganawarsa da shugaban kasar Koriya Kim Jong Un ya ta’alaka kan sakin Amurkawan ba.Trump ya jadada cewa yana kyautata zaton zai zauna da shugaban Koriya ta Arewan farkon watan Yuni.
Yace ina jin idan zaman ba zai zama da amfani ba, ba zamu je ba. Idan naga zaman ba zai tsinana komi ba, sai in nemi ahuwa in fice salum alum.
Shugaban Amurkan ya kuma goyi bayan takwaransa na kasar Japan cewa, ana bukatar ci gaba da matukar matsawa Pyongyang lamba ta daina kera makaman nukiliya.