Shugaban Amurka Donald Trump ya fara daukar mataki kan shirin gabatar da kasafin kudin gwamnatin tarayya, tare da neman yin kari a kudin da ake kashewa kan harkokin tsaro, yayinda yake shirin zaftare kudin da ake kashewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka da wadansu cibiyoyi kamar cibiyar kare muhalli.
WASHINGTON DC —
Jami’an gwammati sun ce fadar White House zata bayyana tsarinta na kashe kudaden gwamnatin tarayya a takardar sanin makamar aiki za’a turawa cibiyoyin gwamnati yau Litinin. Ofishin kasafin kudi da aiwatarwa yace za a fitar da cikakken bayanin tsarin kasafin kudin a tsakiyar watan Maris.
A lokacin da yake yakin neman zabe, Shugaba Trump ya sha yin alkawarin cewa, zai karawa ayyukan sojin kasar karfi, ya kuma bayyana a jawabin da ya gabatar ranar Jumma’a cewa, zai inganta ayyukan soji irinda ba a taba gani ba a tarihin Amurka.
Yace zai nemi a zaftare kudin wadansu ayyuka kamar bangaren kudin fansho da kuma harkokin kula da lafiyar matalauta.