Shugaban Amurka ya Fara Rangadin Kwanaki Hudu a Nahiyar Yammacin Turai

Shugaban Amurka Barack Obama

Irin rawar da kasar Rasha ke takawa a rikicin kasar Ukraine dake gabashin nahiyar turai ya sa shugaban Amurka Barack Obama ya soma rangadin nahiyar yammacin turai domin tabbatar wa kawancen NATO goyon bayan Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama ya fara rangadin kwanaki hudu a turai da zummar sake tabbatarwa kawayen NATO cikakken goyon bayan Amurka, adai dai lokacinda zaman dar dar take karuwa a yankin, saboda irin rawar da Rasha take takawa a rikicinda ake yi a Ukraine.

A duk wunin yau laraba shugaban na Amurka sai gudanar da shawarwari da shugabannin kasashen Estonia da Latvia da Lithuania a babban birnin kasar Estonian. A taron da shugabannin suke yi a birnin Tallinn, mai tazarar kilomita 200 daga iyakarta da Rasha, yana zuwa ne lokacinda ake kara nuna fargaba kan katsalandan da Rasha take yi a rikicin da ake yi a Ukraine, da kuma barazanar da take yiwa kasashen da suke yankin da ake kira Baltics.

Mr. Obama ya kira shawarwarin da zasu yi a yankin da cewa dama ce na sake tabbatarwa kasashen da suka sami ‘yanci bayan wargajewar tarayyar soviet cewa, Amurka zata mutunta yarjejeniyar da aka kulla da ita.

Ana sa ran Mr. Obama zai hadu da shugabannin kasashen da suke cikin kungiyar tsaro ta NATO su 27 domin taron koli da zai maida hankali wajen karfafa irin taimako da kasashen yammacin duniya zasu baiwa Ukraine, yayinda hukumomin kasar da suke kyiv suke ci gaba da fafatawa da ‘yan aware masu biyayya ga muradun Rasha kusa da kan iyakar kasar da Rasha.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban Amurka Barack Obama ya amince a tura karin sojojin Amurka su 350 zuwa Iraqi domin bada kariya ga jami’an difilomasiyyar Amurka a Bagadaza. A dai dai lokacinda mayakan sakai na kungiyar ISIS suka nuna vidiyo na kashe wani ba Amurke dan jarida.

Fadar white House tace ma’aikatar harkokin wajen Amurka ce ta bukaci a tura sojojin kuma ba zasu je fagen yaki ba.