Shugaban Amurka Donald Trump wanda yau Asabar yake kasar Vietnam wurin taron kungiyar tattalin arzikin kasasashen yankin fasific, yace sun tattauna ne akan batutuwa biyu zuwa ukku da shugaban Rasha ViladimirPuttin akan lamari kasar Syria.
Trump ya fadi hakan ne sailin da yake ganawa da manema labarai jim kadan kadan da lokacin da zai bar wurin wannan taron da akayi a Danang akan hanyar sa ta zuwa babban birnin Hanoi fadar gwamnatin kasar ta Vietnam.
Yace bayanar tattaunawar tasu na hadin gwiwa da zasu bayyana wa jama’a zai taimaka kwarai da gaske wajen ceto rayuka da dama.
Kalaman na shugabannin wandanda aka bayar a Kremlin, yace shugabannin sun tabbatar da muhimmacin tabbatar da yin abinda ya dace domin ganin an samar da raguwar tashin hankali a Syria. Cikin matakan ko harda tabbatar da yarjejeniyar rage bude wuta da kuma kawar da kawo wa ayyukan jin kai cikas, sai kuma samar da hanya ta sadidan da zai samar da makomar siyasar kasar mai dorewa.
Haka kuma sanarwan ta amince cewa shugabannin biyu zasu samar da hanyoyin sadarwa tsakanin sojojin su da zai samayi da kariya ga sojojin kasashen biyu, tare da hada gwiwa wajen yaki da kungiyar ISIS.