Shugaban Amurka Barack Obama zai bada shawarar tsuke bakin aljihu

Shugaban Amurka Barack Obama ya fito daga ofishinsa a fadar White House in Washington, 25 Jan 2011

Ana kyautata zaton shugaban Amurka Barack Obama zai gabatar da shawarar tsuke bakin aljihun gwamnati a cikin jawabin da zai yi yau kan halin da kasar ke ciki.

Ana kyautata zaton shugaban Amurka Barack Obama zai gabatar da shawarar tsuke bakin aljihun gwamnati a cikin jawabin da zai yi yau kan halin da kasar ke ciki, da kila ya kwantawa ‘yan jam’iyar Republican a rai wadanda suke kira da a rage kashe kudade domin rage yawan bashin da ake bin kasar. Wani jami’in fadar shugaban kasa ta White House, da ya nemi a saya sunansa, ya shaidawa kafofin watsa labaran Amurka yau Talata cewa, shugaban kasar zai nemi a tsuke bakin aljihu a kasafin kudi na tsawon shekaru biyar kan ayyukan da basu shafi harkokin tsaro ba. ‘Yan jam’iyar Republican da suka sami rinjaye a majalisar wakilai kwanan nan, sun bada fifiko kan rage kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa. Wadansu ‘yan majalisa suna kira da a rage kudin da za a kashe bana da dala miliyan dubu dari . Shugaba Obama zai yi kokarin ci gaba da neman hadin kai da ‘yan jam’iyar Republicans bayan cimma matsaya ba tare da kula da banbancin siyasa ba, kan batun haraji bara. Ana kyautata zato shugaba Obama zai maida hankali kan kalubalar da kasar ke fuskanta cikin jawabin da zai yi yau da dare, da ya hada da samar da ayyukan yi da zuburar da tattalin arzikin kasar.