Shugaban Amurka Barack Obama ya kai ziyara kasar Brazil

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da takwararsa ta kasar Brazil Dilma Rousseff, domin tattaunawa kan dangantakar tattalin arziki.

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da takwararsa ta kasar Brazil Dilma Rousseff, domin tattaunawa kan dangantakar tattalin arziki

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da takwararsa ta kasar Brazil Dilma Rousseff, domin tattaunawa kan dangantakar tattalin arziki. Mr. Obama ya yada zangon farko a Brazil, a ziyarar kwanaki uku da yake yi a kasashen kudancin Amurka, a daidai lokacin da ake daukar matakin soja da zumar murkushe harin da shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi ke kaiwa ‘yan tawaye masu kin jinin gwamnati. Shugaba Obama da sabuwar shugabar kasar Brazil sun hakikanta cewa, ziyarar wata dama ce ta tarihi da zata dora kasashen biyu masu karfin tsarin damokaradiya a yammaci, kan hanyar kulla dangantaka mai karfi. Shugabar Rousseff ta yi kira da a samar da damar cinikayya ta bai daya ga kowa a kuma hada hannu a fannin kimiyya da bincike. Fadar White House ta ce, shugabannin biyu sun yi na’am da yarjejeniyoyi da dama da aka cimma da suka hada da dangantakar harkokin cinikayya da kuma hadin kai a fannin tattalin arziki da sufurin sararin sama.