Shugaban Amurka Barack Obama Ya Ce Kawunan Amurkawa Ba Su Rarrabu Kamar Yadda Wasu Ke Hasashe Ba

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka Barack Obama

A cigaba da karfafa gwiwa ga Amurkawa da Shugaba Barack Obama ke yi tun daga kasar Poland bayan kashe-kashen da aka yi a Amurka, ya sake jaddada cewa Amurka ba ta rarrabu ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya sake karfafa gwiwar Amurkawa, wadanda su ka kadu da abin da shi kansa Obaman ya amsa cewa, al'amari ne mai bakanta rai a matuka a makon, bayan bindige wasu Amurkawa Bakaken fata biyu har lahira da 'yansanda su ka yi da kuma wani kwantan baunan da ya yi sanadin hallakar 'yansanda biyar a Dallas.

Obama ya yi wannan maganar ce a wurin babban taron NATO a Warsaw, to amma ya fi tabo abubuwan da su ka faru a Amurka a taron manema labaran da ya kira. Shugaba Obama zai katse kasancewarsa a Turai din da kwana guda ya dawo birnin Washington da daren yau Lahadi. Ya ce ya na shirin tafiya Dallas a farkon mako mai zuwa bisa gayyatar Magajin Garin Dallas din Mike Rawlings.

An cigaba da zaman dardar a birnin zuwa jiya Asabar; musamman bayan da aka yi ma 'yansandan birnin na Dallas barazana. Wannan barazanar ta sa jami'an 'yansandan sun rufe hedikwatarsu da gine-gine da dama da ke zagaye da wurin, a matsayin shirin ko-ta-kwana, a cewar wani bayanin 'yan sandan.

Daga Poland din, Obama ya fara jawabin nasa ne da abubuwan da su ka biyo bayan harbe-harben da aka yi a Dallas, ya na mai cewa, "Na yi imanin cewa Amurka ba a rabe take kamar yadda wasu ke hasashe ba." Ya ce kasar na da shimfidar da za ta iya dorawa a kai don warware matsalolin da ta ke fuskanta, ciki har da na rashin jituwa tsakanin jami'an tsaro da tsirarun al'ummomi.

Ya ce maharin na Dallas bai wakiltar Bakake, kamar yadda Farar Fatar nan da ya kashe mutane a wata Majami'ar Bakake a Charleston bara bai wakiltar Farar Fata; kuma kamar yadda Ba-Amurken nan Musulmi, wanda ya kashe mutane 49 a Orlando shi ma bai wakiltar Musulmin Amurka.