Shugaba Obama Ya Jaddada Batun Tattalin Arziki Da Ayyukan-Yi

Shugaban Amurka Barack Obama yana jawabin ga zaman hadin guiwar majalisar dokokin Amurka,gameda hali da kasa take ciki.

Shugaban Amurka Barack Obama yace Amurka ta sake yunkurowa na samun ci gaba,ganin kasuwannin sayar da hannayen jari suna bunkasa,ribar da kamfanoni suke samu ya karu,tattalin arziki kuma yana bunkasa.

Shugaban Amurka Barack Obama yace Amurka ta sake yunkurowa na samun ci gaba,ganin kasuwannin sayar da hannayen jari suna bunkasa,ribar da kamfanoni suke samu ya karu,tattalin arziki kuma yana bunkasa.Duk da haka yace tilas Amurka ta zage dantse domin tabbatar da shugabancinta a kasancewa kan sahun gaba a Duniya.

Daya daga cikin matakai na farfado da Amurka shine ta wajen sake gine kayan more rayuwa kamar hanyoyi,da gadoji,hanyoyin dogo na zamani,da kuma yanar Internet mai nagarci.Yace domin janyo hankalin ‘yan kasuwa su bude sabbin masana’antu Amurka tana bukatar kafofin safarar mutane da kaya da bayanai masu inganci.

Yace a Koriya ta kudu suna da hanyoyin shiga Internet masu inagnci fiyeda Amurka.Yace Rasha da Turai suna gina hanyoyi da dogo fiyeda Amurka.Shugaba Obama yace cikin shekaru biyu da suka wuce ta fara daukan matakai sake farfadowa domin ta tafi dai dai da karni na 21.

Yace burin shine ganin nan da shekaru 25 Amurka zata samar da jiragen kasa na zamani masu dan Karen tafiya ga kashi 80 na al’umarta. Yace nan da shekaru biyar kuma Amurka zata zuba jari da zai taimaka wajen ganin kamfanoni sun inganata amfani da woyar celula ga kusan kashi 98 na Amurkawa.