Shugaban Afrika ta Kudu ya isa kasar Libya domin shiga tsakani

Shugaban kasar Afrika ta Kudu yana gaisawa da Firai Ministan kasar Libyai al-Mahmudi Baghdadi al-Mahmudi a birnin Tripoli.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya isa kasar Libya domin shiga tsakani da zumar ganin an daina musayar wuta tsakanin gwamnatin shugaba Moammar Gadhafi da mayakan ‘yan tawaye dake kokarin hambare gwamnatinsa.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya isa kasar Libya domin shiga tsakani da zumar ganin an daina musayar wuta tsakanin gwamnatin shugaba Moammar Gadhafi da mayakan ‘yan tawaye dake kokarin hambare gwamnatinsa. Mr. Zuma ya isa tashar jirgin saman Tripoli babban birnin kasar yau Litinin a ziyararsa ta biyu zuwa Libya tunda yan gwaggwarmaya masu hamayya suka fara zanga-zangar kin jinin Mr. Gadhafi a tsakiyar watan Fabrairu. Fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu tace Mr. Zuma zai wakilci kungiyar hadin kan Afrika a tattaunawar da za a yi da hukumomin kasar Libya kan aiwatar da shawarwarin da Kungiyar Tarayya Afrika ta bayar na warware rikicin kasar Libya. Ofishin Mr. Zuma yace zai nemi a daina dukan amfani da karfin soji, a fadada yankunan da ake kai kayan agajin kasa da kasa a kuma kare lafiyar ‘yan kasashen ketare. Ofishin ya musanta rahotannin dake nuni da cewa, Mr. Zuma zai matsawa Mr. Gadhafi lamba ya sauka daga karagar mulki.