Shugaban Afrika Ta Kudu ya yi bayani na gwalewa saboda yadda rashawa ta yi katutu a jam’iyyar ANC ta kasar mai mulki.
Cyril Ramaphosa, a wata wasika da ya rubuta jiya Lahadi 23 ga watan Agusta, da aka tura wa duk mambobin jam’iyyar ta ANC, ya fara da caccakar batun cece-ku-cen da ake yi akan bada kwangiloli don taimaka wa kasar wajen yaki da cutar coronavirus.
“Abinda ya kawo cece-ku-cen shi ne akwai kamfanoni masu zaman kansu da wasu mutane, ciki har da jami’an gwamnati da suka yi amfani da matsalar kayan asibiti, da zamantakewar al’umma da kuma tattalin arziki don azurta kansu, a cewar wasikar. Ba za a yafe wannan yaudarar ta miliyoyin ‘yan Afrika Ta Kudu ba da yanayin cutar COVID-19 ya shafa, suna fuskantar yunwa a kullum, da rashin ayyukan yi.”
A cikin wasikar Ramaphosa ya kuma rubuta cewa an gano miliyoyin kudin kasar da ya kamata a yi amfani da su wajen inganta fannin sufuri, da samar da abubuwan more rayuwa ga talakawa, da ingantacciyar wutar lantarki, da taimaka wa manoma bakar fata da ke tasowa da kuma bunkasa kasar baki daya, da miyagu suka sace suka sanya a aljihunsu.
Shugaba Ramaphosa ya ce kada jama’a su yi tunanin cewa jam’iyyar ANC wata hanya ce ta samun iko kawai, ko dukiya da fada a ji.