Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma Ya Ce Kasashen Afirka Sun Ruruta Wutar Kyamar Bakin A Kasarsa

  • Ibrahim Garba

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma

Bukin cikar kasar Afirka Ta Kudu shekaru 21 da kafa dimokaradiyya ya zo da caccakar kasashen Afirkan da mutanensu ke dunguma zuwa Afirka Ta Kudu

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya caccaki kasashen da ke sukar kasarsa saboda kashe baki da wasu ‘yan kasar masu kyamar baki su ka yi ta yi. Ya ce ai abin da ya sa ‘yan wasu kasashe ke ta runtuma zuwa kasar shi ne ya na samar da abubuwan more rayuwa sosai ma ‘yan kasar. Ya ce ya kamata masu sukarsa su tambayi kansu ko me ya sa ‘yan kasarsu ke gudu daga kasashensu su na zuwa Afirka Ta Kudun. Ya ce, kodayake a Afirka Ta Kudu aka samu fitinar, amma wasu kasashen Afirka sun taka rawa sosai wajen aukuwarta.

Game da korafin jama’ar kasar na rashin abubuwan more rayuwa isassu kamar yadda aka sa rai, Mr. Zuma ya ce dama ‘yan Afirka Ta Kudu mutane ne masu cike da fushi, kuma hakan, in ji shi, ya samo asali ne daga danniyar mulkin wariyar launin fatar da aka gallaza ma su a baya. Don haka ya ce ya kamata su nemi hanyar da ta dace ta huce fushinsu.

A wannan rahoton na musamman, wanda abokin aikinmu Sahabo Imam Aliyu ya fassara, an lura cewa wannan bikin cikar kasar Afirka Ta Kudu shekaru 21 da samun mulkin dimokaradiyya, inda a nan ne ma Shugaba Zuma ya yi wannan jawabin, ya ga raye-raye da kade-kade da nau’ukan anashuwa iri-iri.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma Ya Ce Kasashen Afirka Sun Ruruta Wutar Kyamar Bakin A Kasar- 2'42''