Shugabannin addini da wakiliyar Muryar Amurka ta tuntuba sun bayyana dalilan da suka kaiga inda ake yau.
Malam Usman Isa Taliyawa mataimakin shugaban kungiyar IZALA yace Allah Ya kan turowa mutane jarabar rashin zaman lafiya sabili da wasu dabi'unsu da halayensu. Cikin munanan halaye da Allah zai yiwa mutum hukunci akwai rashin tausayawa marayu da fakirai ya zama kullum basa barci kuma basu da kwanciyar hankali saboda tunanin rashin abinci da tufafi da dawainiyar yadda zasu yi karatu. Duk lokacin da wadannan basa iya barci domin damuwarsu to Allah kuma zai jarabi al'ummar da yakamata ta dauki nauyinsu. Ita ma zai hanata barci ya hanata wadata.
Haka Allah zai sa mutane su dinga tsoron juna domin rashin amincewa.Duk irin wanna jarabawa ce daga Allah domin an ki kula da marayu da fakirai da sauran nakasassu.
Shi ma Rebaran Dr. Abari Kalla shugaban kungiyar kiristoci reshen jihar Gombe yace a littafinsu an ce zuwa karshen zamani akwai yake-yake da anfani da bama-bamai da sauran abubuwa da zasu dinga tasowa cikin alumma. A fuskar gwamnati idan ba'a mulki da adalci mutane basa cika zaman lafiya. Yace littafi ya nuna cewa idan akwai adali akan mulki jama'a sukan yi walwala da farin ciki. Idan kuma aka samu shugaba mara adalci to jama'a sukan shiga cikin masifa. Irin hakan kan sa wasu su dauka an yi watsi dasu, ba'a kula da bukatunsu ba to dole su tayar da hankali.
Shugabannin sun bada mafita. Malam Usman yace mafita ita ce mutane su gyara halayensu. Shugabannin su fifita bukatun cigaban Najeriya da al'ummarta akan bukatunsu na kansu. Shi ma Rabaran Abari yace mutane su koma ga addu'a. Na biyu gwamnati ta kyautatawa al'umma.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.
Your browser doesn’t support HTML5