Shugaba Trump Ya Sanya Sabbin Takunkumi Ga Kasar Iran

Sabbin takunkumi da Amurka ta sanya, sun zone akan batun nau’ukan kayayyakin da suka hada har da na karafa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa Iran sabbin takunkumi, sa’o’i bayan da shugaban kasar Iran, ya ce ya janye daga yarjejeniyar da aka kula tsakanin kasashe shida, kan makamin nukiliyanta.

A jiya Laraba Trump wanda ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi na kashin kansa, ya ce, zai saka sabbin takunkumi kan nau’ukan kayayyakin da suka hada har da na karafa, wadanda suna daga cikin kayayyakin da suke samawa kasar kudaden shiga.

Takunkumi da Amurka ta sanya, a kan man Fetur din kasar ta Iran, wanda shi ne babban hanyar samun kudin shigar kasar, ya yi mummunan tasiri, a kan tattalin arzikinta.

Fannin sarrafa karafa, ya kasance wata babbar hanya da kasar ke samun kudaden.

Shugaba Trump ya ce, "saboda matakin da muka dauka, yanzu gwamnatin Iran, tana kokarin neman kudin da za ta zuba a fannin, daukan nauyin ayyukan ta'addanci, yayin da tattalin arzikinta, ke ci gaba da shiga cikin matsanancin hali."

Tada jijiyar wuya, da ake yi, tsakanin Iran da Amurka, ya yi kamari a cikin ‘yan kwanakin nan.