Shugaban Amurka Donald Trump na birnin Osaka, a kasar Japan, inda yake halartar wani taron koli da sauran shugabannin kasashen G 20.
WASHINGTON D C —
Taro na farko da ya halarta shi ne wata liyafar aiki da firayin ministan kasar Australia Scott Morrison inda a taron ya ce kasashen biyu kawayen juna ne sosai.
A gefen babban taron kuma, ana sa ran Trump zai yi wasu tarukan, ciki harda ganawa da shugabar Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a yau Alhamis, bayan haka gobe Jumma’a kuma zai gana da shugaban China Xi Jinping.
Ana kuma sa ran Trump zai yi amfani da damar wadannan tarukan na G20 don bayyana cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar ci gaba da sanya takunkumin matsin lamba akan Iran, kuma yana neman ya dakile hanyar samun kudin mai a kasar, ya kuma sa a koma teburin shawarwari akan batun shirin nukiliyar Iran din.