Shugaba Paul Biya Ya Lashe Zaben Kamaru

An ayyana dadadden shugaban kasar Kamaru Paul Biya amatsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar ranar 7 ga watan Oktoba. Sai dai jam’iyyun adawa sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaben, amma Majalisar tsarin mulki ta yi watsi da korafe-korafen a soke zaben.

Clement Atangana, shugaban Majalisar tsarin mulki shine ya karanta sakamakon zaben jiya Litinin.

Kamar yadda sakamakon zaben ya nuna, shugaba Paul Biya ya sami kashi 71 cikin 100 na kuri’un da aka kada. Yayin da abokin takararsa Maurice Kamto, ya sami kashi 14 cikin 100 na kuri’un. Sauran ‘yan takarar bakwai kuma sun sami ‘kasa da kashi 10 cikin 100.

Masu zanga-zanga sun fita cikin fushi sun rera waka dake cewa Paul Biya ya sace nasarar da Maurica Kamto ya samu, amma cikin gaggawa sojoji dauke da makamai suka tarwatsasu.

Sama da shekaru 40 kenan Paul Biya yake shugabanci a Kamaru, shekaru bakwai a matsayin Fara Minista, shekaru 36 a matsayin shugaban kasa. A shekarar 2008 ne ya soke wa’adin da shugaban kasa zai iya yi a kundin tsarin mulki, wanda hakan zai bashi damar yin mulki har sai illa masha Allah.