Shugaba Barack Obama ya ce zai fi mai da hankali kan mayar da hannu agogo baya ga 'yan kungiyar Daular Islama, game da nasarorin da su ka yi a Iraki.
Shugaba Obama ya yi maganar ce da manema labarai a Fadar White House a jiya Alhamis, dab da fara ganawa da tawagar manyan jami'ai na bangaren tsaro don tattauna rikicin Iraki da Syria.
Mr. Obama ya ce Amurka za ta cigaba da kai hare-hare kan wasu takamaimun wurare na Daular Islama a Iraki, ya na mai cewa wannan matakin ya raba mayakan sa kan da makamansu da kuma sauran kayan aikinsu.
To amma Shugaba Obama ya ce bayan wannan bai da wata dabara a kasa ta tinkarar mayakan sa kan a halin yanzu, sabanin cewa da ake ta yi wai ana gab da kai hari kan 'yan Daular Islama a Syria.
Shugaba Obama ya ce 'yan Daular ta Islama sun sami mafaka a Syria, kuma sojojin na Syria ba su iya zuwa wuraren da ke karkashin ikonsu.