Shugaba Obama da Hillary Clinton Sun Kaddamar da Kemfen Tare a Jihar North Carolina

Hillary Clinton da Shugaba Obama

Shugaba Barack Obama da tsohuwar abokiyar hamayyarsa , wato Hillary Clinton da yanzu take neman ta gajeshi, sun hada karfi da karfe sun kaddamar da kemfen tare a jihar North Carolina.

Shugaba Obama yana son Hillary ta gajeshi domin ta kare ayyukan da ya yi da kuma tabbatar ta dorawa akan abubuwan da ya yi.

A jawabinsa, Shugaba Obama ya jaddada dalilan da suka ya zama wajibi Hillary Clinton ta zamo shugaba ta 45 da zata ja ragamar mulkin kasar.

Shugaban yace "na tsuma kuma Hillary ta tsumani saboda haka ashirye nake na yi aiki tukuru" inji Obama yayinda yake yiwa dimbin magoya bayansu jawabi a gangamin da suka yi a birnin Charlotte dake jihar North Carolina jiya Talata.

Hillary Clinton da magoya bayanta

Obama ya gabatar da Hillary Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar a matsayin mace mai kwakwalwa, mai hazaka, wadda kuma ta fi kowa cancanta ta zama shugabar kasa. Yace Hillary shugaba ce mai zuciya da karfin hali amma kuma mai jin tausayi wadda zata kare kasar. Zata taimaki iyalai ta kuma kare muradun Amurka.

Shugaba Obama yace zata san yadda zata samu goyon bayan kasashen duniya akan muradunmu yaynda kuma zata tabbatar sauran kasashen su ma sun tashi tsaye sun yi abun da yakamata. Sai Obama yace "dalilan ke nan da suka sa ta cancanci ta zama shugabar kasar Amurka" injishi.

Har yanzu Shugaba Obama nada matukar farin jini kuma goyon bayan da ya ba Hillary Clinton zai taimaka matuka.