Shugaba Obama da Frayin Ministan Isra'ila Sun kammala Ganawa, Sai Dai...

A wan nan hoto shugaban Amurka Barack Obama ne da Frayin Ministan isra'ila Benjamin netanyahu.

Shugaba Barack Obama na Amurka da friministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun kammala tattaunawar da suka yi a fadar shugaban Amurka ta White House a yau juma’a.

Shugaba Barack Obama na Amurka da friministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun kammala tattaunawar da suka yi a fadar shugaban Amurka ta White House a yau juma’a, amma dukkansu biyun sun ce har yanzu basu sami kaiwa ga kauda bambance-bambancen dake tsakanin su game da manufar Amurka kan yankin gabas na tsakiya ba.

Tattaunaware tazo ne kwana guda da muhimmin jawabin da shugaba Barack Obama yayi na kalubalantar ci gaba da mamayen da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasdinawa da batun shata kan iyaka tsakanin Isra’ila da kasar da ake kokarin samarwa Falasdinawa tasu ta kansu.

A jawabin da shugaba Obama ya yiwa kasa jiya Alhamis, yayi bayanin dalla-dallar manufar Gwamnatinsa na goyon bayan da Amurka ke baiwa Isra’ila yace babu wata tantama, amma kuma yayi kiran da ayi amfani da kan iyakokin da ake dasu kafin yakin Isra’ila da larabawa a shekarar 1967 domin baiwa falasdinawa kasarsu tunda dukkan sassan biyu sun amince da musayar yankunan kan iyakar da bangarori biyun suka shata.

Sai dai friministan isra’ila Benjamin Netanyahu yayi watsi da wannan jawabi na shugaba Barack Obama, yace ba yadda za’a yi Isra’ila ta yarda a sake komawa ga shacin kan iyaka kafin yakin shekarar 1967, domin janyewar Isra’ila daga wasu yankunan da yanzu take mamaye dasu zai janyo cikas ke nan ga zaman Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a Yammacin Kogin Jordan dake a wajen Isra’ila.

Duk da haka a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan tattaunawar ta yau Juma’a, Mr. Netanyahu yace a shirye Isra’ila take da tayi sassauci kan wasu abubuwan, amma banda batun sake komawa ga kan iyakoki kafin yakin Isra’ila da larabawa a shekarar 1967.

http://maps.google.com/maps/ms?ie=UTF8&hl=en&msa=0&msid=211952108644978982102.0004a2d8392da4fc54c26&ll=45.761543,31.464844&spn=20.030061,-143.4375&output=embed
View President Obama's Europe Trip and G8 Summit in a larger map