Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddamar Da Babbar Matatar Mai Ta Dangote A Legas

Matatar Man Fetur Ta Dangote

Ana sa ran fara aikin wannan matatar Mai zai haifar da gagarumin tasiri ga tattalin arzikin Najeriya da kuma rayuwar 'yan kasar.

A halin yanzu dai Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da arzikin Man Fetur a nahiyar Afirka, amma duk da haka ta dogara kacokan kan shigo da taceccen mai daga kasashen waje domin biyan bukatunta na cikin gida.

Kasar dai na kokawa da kalubalen rashin isassun kayan aikin tace mai a cikin gida, lamarin da ya janyo raguwar kudaden da take samu daga kasashen waje da kuma jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali, sakamakon tabarbarewar farashin man a duniya.

Matatar Man Dangote da ke yankin Lekki na jihar Legas, ana sa ran za ta sauya wannan lamari ta hanyar karfin tace ganga 650,000 a kowace rana, wadanda suka hada da man fetur da dizal da man jiragen sama, da sauran su.

Haka kuma, matatar Man za ta samar da damarmaki iri-iri ga ma’aikata na cikin gida, inda ake sa ran za a samar da ayyukan yi kai tsaye har 70,000 a lokacin aikin gini da na aiki.

An tsara matatar Man Dangote ta dace da yanayin muhalli a duniya, tare da na’urori na zamani da fasahar da za su taimaka wajen rage fitar da iskar Carbon.

Ana kuma sa ran cewa matatar za ta kawo sauyi ga masana’antar Man fetur da iskar gas ta Najeriya, domin hakan zai sa kasar ta zama kasa mai fitar da Man fetur da kuma bunkasa matsayinta a kasuwar makamashi ta duniya.

Wannan aiki dai wani muhimmin mataki ne na bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma dogaro da kai, domin zai rage dogaro da Man fetur da ake shigowa da shi daga waje da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati.

Ana sa ran matatar dangote za ta kafa sabon ma'auni ga masana'antar tace matatar mai a Afirka da ma sauran su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da ita a ranar 22 ga Mayu, 2023, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasa a fannin kimiyya ta zamani, Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi 7 ga watan Mayu, 2023.