Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gana Da Firayim Ministan Kasar Denmark A Washington

  • Ladan Ayawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Firayim Ministan Britaniya David Cameron a Taron G7, Munich, Yuni 8, 2015.

A daidai lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ke ci gaba da ziyarar aiki a nan Birnin Washington, DC, mai ba shi shawara na musamman a fannin yada labarai Femi Adesina ya gabatar da wata sanarwar cewa:

A wata ganawar da Shugaba Muhammadu Buhari yayi da Firayim Ministan kasar Denmark Mr. Lars Rasmussen a nan birnin Washington DC, ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen daukan gagarumin matakin rage yawan kudaden da Najeriya ke kashewa akan sayen kayan abinci daga kasashen waje, sannan kuma ya kara tabbatar da kudirin gwamnatin shi na gaggauta raba hannun bunkasa tattalin arzkin Najeriya ta hanyoyi daban-daban.

A shekarun baya, inji shugaba Buhari mun bari dama ta kubuce mana, ba mu raba hannu wajen bunkasa tattalin arzikin mu ba saboda a lokacin mun dogara ne akan hanya kwaya daya tilo.

Shugaba Mahamadu Buhari ya ce :"Mu na iya bunkasa noma da albarkatun karkashin kasa sosai. Yanzu za mu yi amfani da wadannan matuka. Gyara yadda a baya aka yi watsi da wadannan fannoni guda biyu, zai taimaka wajen rage yawan rashin ayyukan yi kuma kasar mu za ta kara bunkasa ta zama mai arziki da amfani."

Za mu yi na'am da karin zuba jari a fannin noman mu da kuma albarkatun karkashin kasa daga kasashen dake da kwarewa. Shugaba Buhari ya ce saboda mai muka yi watsi da su, amma yanzu dole mu koma mu su.

Shugaba Buhari ya gayawa Rasmussen cewa:' Mu na kashe kudade masu yawan gaske wajen sayen abinci da abubuwan da ake sarrafawa da madara daga kasashen waje. Mu na so mu rage wannan ta hanyar bunkasa na mu albarkatun da muke da su a kasar mu.'

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da Firayim Ministan na kasar Denmark cewa gwamnatin tarayyar Najeriya za ta ci gaba da aikin hadin guiwa da sauran kasashe domin ta kara kyautata tsaro a ruwan tekun mashigin Guinea.

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatin shi ta yi tsayin daka wajen kawo karshen babbar asarar kudaden shiga da take tafkawa sanadiyar satar danyen man da ake yi, sannan kuma ya ce kasashen duniya sun tabbatarwa da gwamnatin shi cewa za su taimaka wajen dak'ile fitar da lodin danyen mai ta barauniyar hanya.

Daga karshe, kamar yadda yake rubuce a cikin sanarwar da Femi Adesina ya gabatar, Firayim Ministan kasar Denmark Mr.Rasmussen ya godewa shugaba Buhari sannan ya ce su na da kwarewa sosai a fannin noma , kuma ya ce za su iya taimakawa sosai a wannan fanni.

Halima Djimrao ce ta gabatar darahoton 4'05

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gana Da Firayim Ministan Kasar Denmark A Washington 4'05