Shugaban ya baiwa ministocin sa da wasu kusoshin gwamnatin umurni sunyi anfani da kundin kasafin kudi na wannan shekarar da aka mika musu domin tantancewa da kuma tabbatar da cewa abinda aka kudurta a rubuta tun farko shine a zayyane.
Wato ba ayi wani aringizo ko wani abu mai muhimmacin canza rayuwar ‘yan Najeriya bisa tsare-tsaren canji da gwamnatin sa ta gabatar ba.
Akan haka ne wakilin sashen Hausa Umar Faruk ya tuntubi wani kwararre a shaanin tattalin arziki daga jamiaar Abuja, wato Farfesa Nazifi Darma.
Umar kuma ya tambaye shi ne ko baya ganin cewa wannan jinkirin ko wannan umurnin ba zai ci gaba da kawo cikas akan manufofi ko zakuwar ‘yan Najeriya su fara cin moriyar mulkin na shugaba Muhammadu Buhari ba?
Ga kuma abinda farfesan ya shaidawa Umar
‘’Gaskiya wannan shawarar dashi mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya dauka cewa ko wane minister a bashi kofi na kasafin kudin da ya shafi maaikatar sa yaje ya zauna ya duba cikin tsanaki ya tabbatar cewa ba ayi aringizo ko wani abu na cuta ba gaskiya ko wane jinkiri za ayi na sati daya ko biyu a tabbatar cewa abinda aka kai da kuma abinda akayi niyyar za a aiwatar yayi dai-dai abu ne mai kyau saboda mun sha fada cewa mafi yawancin rashin gaskiya da al’mundahana da ake a kasar nan ta hanyar kasafin kudi ne, to idan ya zama cewa an dauki wannan mataki to kaga anyi maganin dukkan wani mai tunanen yasa wasu abubuwa cikin kasafin kudi daga baya a koma aje ayi sata wannan yayi dai-dai, kuma muna yin anfani da wanna damar domin kara ba ‘yan Najeriya hankuri cewa lallai wannan canji da akayi idan dai har ana son ayi wa jamma aiki ayi maganin sata gaskiya wadannanmatakan sunyi dai-dai, sai mu kara hankuri kafin mu gani a kasa.’’
Ga Umar Faruk Musa da ci gaban rahoton 3’32
Your browser doesn’t support HTML5