Ziyarar da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai jihar Zamfara ta soma ne ta kuma karkare a fadar gwamnan jihar inda shugaban ya yiwa sarakunan gaegajiya da shugabannin addini da na siyasa jawabi.
Bayan ya jajantawa gwamnati da jama'ar jihar akan dimbin tashe tashen hankula da suka yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi, Shugaba Buhari ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa da yin aiki tukuru domin samar da tsaro da kuma zaman lafiya.
Dangane da wannan ziyarar, wasu sun tofa albarkacin bakinsu. Gwamnan jihar ya ce sun sha fama da tashe tshen hankali a jihar amma shugaban kasa bai taba kawo masu ziyara ba sai wannan karon. Ya ce sun yaba da ziyarar.
Inji Gwamnan na Zamfara, shugaban kasa ya ji abubuwan da mutane suka fada da matsalolin da suke fuskanta. Ya ji kuma ya nuna za'a dauki matakan magance su. Nan take ya ba hafsoshin sojojin tsaro cewa dole ne a kawo karshen tashin hankali a jihar.
Amma a wani bangaren wasu na ganin shugaban kasar ya makara idan aka yi la'akari da ukubar da 'yan jihar suka sha sanadiyar hare hare, da kashe-kashe, sace mutane da fashi da makami. Dr Suleiman Sha'aibu Shinkafi, dan asalin jihar kuma dan kungiyar Amnesty International, ya ce ziyarar ta siyasa ce idan kuma ya zo jaje ne ya makara. Ya ce da suna ganin suna da Buhari amma yanzu sun gane basu da kowa sai Allah. Wanna ziyarar ma bai je koina ba sai gidan gwamnati.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5